Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Haramta Zabukan Shugabannin APC A Karkashin Kwamitin Riko Na Buni - PDP


APC, PDP
APC, PDP

“A karkashin jagorancin Mai Mala Buni, jam’iyyar APC ba ta da shugabanni na kasa, haka kuma duk wasu taruka da zaben shugabanni da aka gudanar a karkashinsu ba halatacce ba ne.”

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta soma gudanar da tarukan zaben shugabancin jam’iyyar, tare da zabukan shugabannin gundumomi na jam’iyyar a ranar Assabar.

To sai dai akwai rahotannin samun cece-kuce da tankiya har ma da yamutsi a wurare daban-daban na kasar.

A yayin da wasu wurare aka ruwaito cewa bangarori masu takaddama da juna sun gudanar da zabe daban-daban fiye da daya a mazaba guda, wasu wuraren kuma rikicin ne ya barke har ma da baiwa hammata iska.

Gwamna Mai Mala Buni
Gwamna Mai Mala Buni

To amma kuma jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi da’awar cewa zaben bai halatta ba, idan aka yi la’akari da hukuncin kotun kolin kasar akan shari’ar zaben gwamnan jihar Ondo.

Wata sanarwa da sakataren watsa labaran jam’iyyar ta PDP na kasa, Kola Ologbodiyan ya fitar, ta bayyana cewa hukuncin kotun koli akan zaben gwamnan jihar Ondo, ya haramta kwamitin shugabancin rikon kwarya na APC a karkashin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.

Akan haka jam’iyyar ta PDP ta ke ganin cewa dukan zabukan da kwamitin riko na Mai Mala Buni ya gudanar da wadanda zai gudanar, ba su hallata ba ta fuskar doka.

PDP ta zargi gwamnan da suran shugabannin APC da “yaudarar ‘yan Najeriya ta hanyar jefa su a haramtattun zabuka da kuma suka haifar da rikicin da tashe-tashen hankula, alhali sun sani cewa sun kauce wa hanyar doka.”

Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP
Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP

Jam’iyyar ta PDP ta kafa hujja da sashe na 183 na kundin tsarin mulkin Najeriya, da kuma sashe na 17(4) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC da kotun koli ta yi amfani da su wajen saka ayar tambaya akan halaccin kwamitin rikon na Mai Mala Buni.

A cewar PDP, sashe na 183 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, ya haramtawa duk wani gwamna da ke kan mulki, ya rike wani mukami a yayin da yake kan kujerar gwamna, a yayin da sashen na 17(4) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC kuma, ya bayyana karara cewa “ba wani shugaba a kowane sashe na jam’iyyar da zai rike wani mukami na zartarwa a gwamnati a lokaci daya.”

Ta kara da cewa “a karkashin jagorancin Mai Mala Buni, jam’iyyar APC ba ta da shugabanni na kasa, haka kuma duk wasu taruka da zaben shugabanni da aka gudanar a karkashinsu ba halatacce ba ne.”

To sai dai a martanin da ta mayar, jam’iyyar APC ta yi watsi da da’awar PDP.

A wata sanarwa da sakataren rikon kwarya na kwamitin shirya babban taron jam’iyyar APC, Sanata John Akpanudoedehe ya fitar, jam’iyyar ta bayyana ikirarin na PDP a matsayin maras tushe balle makama.

Yanzu haka dai jam’iyyar ta APC tana shirye-shiryen ci gaba da gudanar taruka da zaben shugabanni na gaba amatakan jihohi da kuma kasa baki daya.

XS
SM
MD
LG