Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar ICPC Ta Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Jama’a A Jihar Plateau


Sonni Tyoden mataimakin gwamnan jihar Plateau
Sonni Tyoden mataimakin gwamnan jihar Plateau

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ICPC, ta gudanar da taron wayar da kan jama’a kan matakan hana cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma musamman a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu.

Taken taron dai shine “Yin Gaskiya Ginshikin Yin Shugabanci Mai Inganci Da Ci Gaba” ya tattaro masu ruwa da tsaki da kusoshin gwamnati da kuma shugabannin shugabannin kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ekpo Nta, yace makasudin taron shine su samar da kamfen din yaki da cin hanci da rashawa a jihohi sabanin yadda jama’a ke kallon yakin a matsayin hakkin gwamnatin tarayya ne kawai.

Mr. Nta, yace idan jihohi sun bi matakan da gwamnatin tarayya ke bi wajen bankado gurbatattun shugabanni dake cin hanci da karbar rashawa, zasu magance yawan matsalolin dake damunsu don samun ci gaba da inganta rayuwar al’umma da kuma samar da abubuwan more rayuwa.

Yace a karshen taron na wayar da kan jama’a jihohi zasu iya auna nasarar da suka samu wajen rage yawaitar rashin aikin yi, sanadin rashin bin ka’ida wajen rarraba mukamai da wasu batutuwan da suka sabawa doka. Mr. Nta, yace hukumar yaki da cin hanci da rashawa tana da hakki da dama da tilasta yin abin da ya dace, gurfanar da masu laifi da kuma hana duk wani laifi da ya shafi cin hanci da rashawa.

Mataimakin gwamnan jihar Plateau Farfesa Sonni Tyoden, yace taron yazo ne akan ka’ida domin anyi shine domin wayarwa da mutane kai.

Hukumar cin hanci da rashawa dai ta zabi jihar Plateau ta kasance gurin da zata wayar da kan ‘daukacin al’ummar Arewa ta Tsakiyar Najeriya kan fa’idar dake tattare da aikata gaskiya don gunadar da shugabanci na gari.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG