Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Clinton Ta Gana Da Shugabar Demokuradiyya Aung San Suu Kyi


Shugabar 'Yan hamayya a Burma Aung San Suu Kyi, da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Rodham Clinton.
Shugabar 'Yan hamayya a Burma Aung San Suu Kyi, da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Rodham Clinton.

A yau jumma a ranar karshe a ziyarar kwana uku da zai shiga tarihi da ta kai kasar Burma, sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tayi shawarwarin gaske da shugabar rajin Demokuradiyya kasar Burma Aung San Suu Kyi.

A yau jumma a ranar karshe a ziyarar kwana uku da zai shiga tarihi da ta kai kasar Burma, sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tayi shawarwarin gaske da shugabar rajin Demokuradiyya kasar Burma Aung San Suu Kyi, a birnin Rangoon.

Bayan ganawarsu a gidan shugabar wacce take da lambar yabo ta Nobel, a gidan da cikin shekaru fiyeda ashirin hukumomin kasar suka yi mata daurin talala, Madam Clinton da Aung San Suu Kyi suka fito a varanda suna rike da hanu yayinda suke zantawa da manema labarai.

Sakatariya Clinton ta yabawa Aung San Suu Kyi “sabo da akida da tsinkaya a shugabanci, tace Amurka tana son ganin ana hulda da kasar Burma cikin mutunci da sauran kasashen duniya. Madam Clinton tace Aung San Suu Kyi a bar koyi ce.

Da take magana shugabar rajin demokuradiyyar Aung San Suu kyi ta bayyana farin cikin ganin yadda Amurka take tuntubar Burma, ta kara da cewa hakan zai saukakawa kasar a shirye shiryen mulkin Demokuradiyya.

Babu daya daga cikin matan biyu da ta ambaci batun takunkumi mai tsanani da aka kakakbawa kasar, sai dai an ni sakatariya Clinton tana fadi jiya Alhamis lokacin da ta kai ziyara babban birnin kasar Naypidaw cewa ana sa ido sosai domin nazarin dukkan matakn sauye sauye da kasar take dauka ta fuskar demokuradiyya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurkan tayi magana d a manem alabarai bayan ganawa wacce ake yi wa kallon ta tarihi da shugaban kasar Thein Sein, wadda yake jagorancin canje canje da kasar take yi tun da ya kama mulki cikin watan Maris. Shugaban wadda tsohon soja ne yay aba da sabon babi da aka bude a dangantaka da Amurka.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG