Tsadar kayan masarufi, musanman bayan cire tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi tun watan Mayu, ya sa shirye-shiryen bukuwan Kirsimeti sun zo wa 'yan Najeriya cikin kunci.
Kamar yadda aka saba a daidai irin wannan lokaci a kowacce shekara, Kiristoci a Najeriya na shirye-shiryen in da kasuwanni a sassan kasar kan cika makil da masu saye-da sayarwa.
A bana al’amarin ya sauya sosai; masu saye suna kokawa kan karancin kudade a hannu da kuma tsadar kayaiyaki, baya ga haka masu sayarwa suna koka wa rashin ciniki.
Muryar Amurka ta halarci kasuwan Jos, babban birnin Jihar Filato inda ta yi hira ta masu saye da sayarwa.
Sarah Agado wadda ta zo sayan kayyayakin biki, ta yi murnan wannan lokaci amma ta koka akan kasawarta na sayan wasu ababe.
‘’Kirsimeti kam ta gabato amma abubuwa yayi zafi; an dan siyawa yara kaya amma babu sauran abubuwan kamar takalma. Ba a iya saya ba domin mai yayi wahala; komai yayi tsada. Ba mu iya sayawa yara abubuwan da yakamata ba'’, kuma “kukan mu shine a saukar mana da kudin mai. In mai yayi sauki, komai zai canja.” in ji ta.
Lami da Talatu suma sun halarci kasuwan domin sayan kayan biki sun kuma koka da hauhawar kaya sanadiyar cire tallafin mai da gwamnati ta yi.
“Tunda aka cire mana talafin mai din nan abubuwa suka zama da wahala. Kudin mota damuwa ne; abinci damuwa ne; masara da muke saya dari da hamsin, dari biyu; dari uku, yanzu na sayi masara da aka yi girbi Nera dari biyar, dari shidda. Ka ga babu sauki’’, in ji Lami.
Ita kuma Talatu ta ce “Muna jin dadi shekarun da su ka wuce, amma da aka cire tallafin mai, mun samu damuwa komai ya karu;yayi tsada’’ kuma '‘gwamnati ya duba ya taimaki talakoki. Talakoki ba karamin wahala suke sha ba''.
Haka zalika, Bitrus Pede, shi ma ya koka da mawuyaccin hali da cire tallfin mai ta jefa 'yaan kasar a ciki, yana cewa ‘’Kirsimetin bana akwai dan wuya. Da aka cire tallafin mai, abubuwa kawai sun yi mana wuya; abubuwa sun yi tsada. Shinkafa da muka saba saya dubu daya, yanzu ya koma dubu daya da dari biyar. Kazan agric yakan kai dubu goma. Fakitin Maggi ma yanzu sai haurawa. Rigan da zaka dan saya ma yaro, malam, lamarin sai addu’a.’’
Suma dillalai da ’yan kasuwa, lamarin ya shafe su, inda sai kukan rashin ciniki sukeyi
‘’Wannan shekarar mutane na kukan kudi sabo da haka babu ciniki. Kai ma ka gani. Ka yi fiye da mintuna goma a nan, ka ga wani ya zo ya taya abu a nan? Mutane na so su sayi kaya amma rashin kudi ya hana su. Muna jin zafin haka’’ in ji Cyprian Okoye.
A baya bayan nan ne Hukumar Kididdiga Ta Kasa a Najeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki a kasar ya kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da kasar ta ga hakan tun a shekarar 1996.
Dandalin Mu Tattauna