Hukumar ta ce farashin kayaki yayi matukar tashi a watan Junairun shekarar nan, inda farashin ya karu da kaso 8.8 cikin dari, idan aka kwatanta da yadda farashin yake a watan Janairun shekarar 2023.
Rahoton ya ce farashin kayayyaki sun cigaba da hauhauwa a farkon shekarar da aka shiga, fiye da yadda farashin yake a watan Disambar shekarar da ta gabata.
Hukumar NBS ta ce, farashin kayakin abinci a Najeriya yayi matukar tashi a watan Janairun da ta gabata, inda farashin ya karu kuma ya kai kaso 35.41 cikin dari bisa ma'auni, wanda hakan ya nuna cewa farashin ya karu da kaso 11.10 cikin dari, idan aka kwatanta da yadda yake a watan Janairun shekarar 2023, inda farashin yake a matsayin kaso 24.32 cikin dari.
Farashin kayakin masarufi da sauran nau'ukan kayayyaki sun cigaba da hauhauwa a kasar biyo bayan cire tallafin man-fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi lokacin kama rantsuwar aiki.
Hauhawar farashin kayaki a Najeriya ya zamo wani abu da 'yan kasar ke ta kokawa akayi, wanda kuma hakan yasa wasu ke rayuwa da abin kalace sau daya a yini.
A hirarsa da Muryar Amurka, Nasiru Shu'aibu Marmara masani kuma manazarci kan lamuran da suka shafi tattalin arziki da cigaban kasa, ya ce "yadda farashin kayayyaki yake tashi a Najeriya, babban barazana ne ga tattalin arzikin kasar, duk da cewa anyi hasashen faruwar hakan, idan aka duba yadda aka daura tubalin tafiyar da tattalin arzikin kasar."
Nasiru Shu'aibu ya kara da cewa "Gwamnati yanzu tana kokarin ganin ta kara samar da hanyar kudin shiga ga yan kasar, domin yazo dai-dai da yadda farashin kaya yake a kasar."
Yanzu dai hankulan yan kasar ya karkata ne ga mahukunta, domin ganin yadda zasu shawo kan lamarin.
Saurari rahoton Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna