Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Bam Ya Hallaka Mutane 5 Da Jikkata 11 A Mogadishu


Wani harin bam din da aka kai ta wata mota ya hallaka mutane 5 ya kuma raunata wasu 11 a wajen wani wurin duba ababen hawa da ke daura da Fadar Shugaban Kasa a Mogadishu, babban birnin Somaliya jiya Talata.

Wani mai magana da yawun gwamnatin yankin ya ce harin bam din ya auku ne a harabar babban dandalin kasa. Ya ce uku daga cikin wadanda su ka mutu din sojoji ne.

Kungiyar al-Shabab mai tsattsauran ra'ayin addini ta dau alhakin kai harin. Wannan kungiya mai alaka da al-Qaida, ta kai hare hare da dama a birnin na Mogadishu, ciki har da harin bama-bamai da bindigogi kan otal-otal da wuraren cin abinci da jami'an gwamnati su ka fi zuwa.

Kungiyar ta'adda ta al-Shabab, na daya daga cikin manyan kalubalolin da sabon Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Mohammed, ya ke fuskanta.

Mayakan na al-Shabab, sun ayyana shi a zaman wanda ya yi ridda, suna masu gargadin 'yan Somalaiya, cewa kar fa su ba shi goyon baya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG