Jirgin mallakar South Sudan Supreme airline, sunce mutane 21, dake cikin jirgin duk sun tsira, lokacin da yake kokarin sauka, sai dai mutanen suna asibitin Wau, domin karbar maganin rauni da suka samu.
Wani Injiniya a filin jirgin saman na Wau, mai suna Paul Charles, yace jirgin yayi kokarin sauka ne a lokacin yanayi mara kyau sai yayi karo da wata babbar mota dake tsaye kan hanyar saukar sa.
Charles, yace yanayi ne babu kyau, kamar yadda direban jirgin ya bayyana, yace bai ganin wuri sosai akan hanyar saukar tasa.
Sai dai jirgin ya kama da wuta sa’ilin da yayi wannan mummunar saukar.
Ministan yada labarai na jihar Wau, Mr Bona Gaudensio, ya tabbatar cewa mutanen dake cikin jirgin sun samu rauni amma kuma baiyi wani Karin haske game da halin da suke ciki ba.
Sai dai ya shaidawa muryar Amurka cewa bai wuce sa’a daya zuwa biyu ba da aka kawo wadannan mutanen asibiti ba “idan mun tantance halin da suke ciki zamu sanar da mutane ta kafar yada labarai.”
Facebook Forum