Wata jarida ce ta zargi tsohon daraktan fadar shugaban kasa kuma ministan kudi a gwamnatin dake ci yanzu, wato Hashim Masaudu da cewa ya fitar a yayin wani cikinikin boye na tan dubu biyar na karfen uranium.
Majalisar ta ba kwamitin wa'adin kwanaki arba'in da biyar ya kammala aikinsa ya kuma gabatarwa majalisar rahotonsa.
Onarebul Iro Sani shi ne mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar yana mai cewa majalisa tana son ta san gaskiya da karya dangane da zargin dalili ke nan da ta kafa kwamiti ya binciki lamarin, ya bata ainihin gaskiya kana ita kuma ta san irin matakan da zata dauka, injishi. .
Amma wasu 'yan kasar Nijar na ganin kwamitin zai ci karo da kalubalen da ka iya dabaibaye binciken. Editan jaridar Letan nada irin wannan ra'ayin. Yace a lokacin da Hashim Masudu yayi magana akan zargin yace shugaban kasa ne ya turashi. Yace da zara ya ambaci shugaban kasa basu da tayi illa su tunkari shugaban kasan. To saidai babu wata doka da ta basu ikon tunkarar shugaban kasa, injishi.
Wata matsala ta biyu ita ce shi kwamitin bashi da hanyar da zai binciki kamfani a kasashen waje kuma cikin su goman babu lauya ko akanta da ya san harkar kudi.
Dan majalisar kasa Onarebul Mammadu ya ja hankalin takwarorinsa akan maganar rikon amana. Yace idan al'ummar kasar suna jira a samu gaskiyar maganar dole shugaban majalisa ya taimaka a samo ma kwamitin abubuwa da hanyar da zai yi aikinsa cikin kwanakin da aka bashi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum