Yace “na samu labarin abin bakin cikin da ya faru jiya a wajen da ruwan Kintampo ke kwarara, ina mika taaziyya ta ga ‘yan uwan wadannan mutanen game da wannan abin bakin ciki”
Shugaba Nana Akufo Addo, ya aike da wannan sakonne a shafin sa na Twitter a jiya littini. Wannan itace da aka bayyana mai girman gaske ya fadi ne lokacin da akayi tsawa a wannan wurin da ruwan Kintampo, ke kwarara, wannan wuri dai sanannen wuri ne da ake zuwa yawon bude ido, dake gundumar Brong Ahafo, dake tsakiyar Ghana.
Itacen ya fada wa wasu mutane dake cikin tafki suna wanka a wannan wurin yawon bude ido.
Ko baya ga mutane 18, da suka mutu, haka kuma an kai wasu 20 asibiti domin yi musu magani, inji Desmond Owusu Boampong, wanda jami’in dan sanda ne.
Yawancin wadanda suka mutu dai galibi dalibai ne daga makarantar Wenchi Methodist, Secondary school, da kuma daliban jami’ar Samar da makamashi da albarkatun kasa wato University of Energy and Natural Resourses.
Kitampo, yace an fara binciken musabbabin afkuwar faduwar wannan itace amma dai bayanan farko sun nuna cewa ikon ALLAH ne.
Facebook Forum