Kwamishanan 'yansandan jihar Borno Mr. Daniel Chukwu ya tabbatar da mutuwar mutane goma sha shida da suka hada da maharan guda bakwai tare da wasu goma sha uku da suka jikata.
Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da 'yan kunar bakin wake su bakwai a hare-haren kunar bakin wake da aka kai a wurare daban daban har biyar a birnin Maiduguri.
Guda goma sha ukun da suka samu raunuka ana yi masu jinya a wasu asibitoci.
Kwamishanan yace maharan sun kai hare-haren ne a wurare daban daban da suka hada da Jami'ar Maiduguri da unguwar Kalari da Zannari da dai sauransu inda aka samu salwantar rayuka.
Inji kwamishanan dan kunar bakin wake na farko ya je Jami'ar Maiduguri ne inda ya tada bam din dake jikinsa a wajen ofishin masu tsaron Jami'ar. A harin ya kashe kansa da kansa da mutum daya tare da raunata wasu mutane uku.
A cikin daren jiyan ne da misalin wajen karfe goma sha biyu aka samu tashin tagwayen bamabamai a unguwar Zannari cikin Maiduguri. Nan ne wasu 'yan kunar bakin wake biyu suka shiga wani gida kana suka tada bamabaman dake jikinsu suka kashe mutanen gidan su takwas da su kansu 'yan kunar bakin waken yayinda wasu goma sha daya suka samu raunuka.
Bam na uku ya tashi ne a Zannarin sai dai dan kunar bakin waken ne kadai ya mutu.
An kama 'yar kunar bakin waken ta hudu a raye a unguwar Zannarin amma daga baya ta mutu ba tare da an samu an tantance inda ta fito ba.
Da safiyar yau 'yan kunar bakin wake biyu sun shiga harabar Jami'ar Maiduguri inda suka kashe kansu da kansu ba tare da taba kowa ba.
Tuni 'yansanda suka tura jami'an tsaro a wuraren inda suka dauki matakan tsaro.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum