Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Wanda Yake Kiran Masifa Bai Santa Ba Ne -Gwamnan Borno


Gwamnan Borno Kashim Shettima daga hagu tare da hafsan sojojin Najeriya Janar Buratai
Gwamnan Borno Kashim Shettima daga hagu tare da hafsan sojojin Najeriya Janar Buratai

A matsayinsa na shuagaban kungiyyar gwamnonnin Arewa 19 yace yana ganin wadanda suka ba matane wa'adin ficewa daga kasarmu suna neman su tada fitina basu san yaki ba ne idan ba haka ba matasan arewa ba zasu yi furucin da suka yi ba

Akan fadin ra'ayi gwamnan Borno Kashim Shetima yace akwai banbanci da kokarin tada fitina kamar yadda matasan Arewa suke neman yi da bayyana ra'ayi.

Gwamnan ya cigaba da cewa duk wanda yake neman tada zaune tsaye bai san tashin hankali ko yaki ba ne. Yana mai cewa duk wanda ya san yaki ba zai yi irin kalamun da matasan arewa suka yi ba na cewa kabilar Igbo su bar jihohin arewa nan da watanni uku.

Acewar gwamna Shettima yau idan akwai wanda ya fi kowa sanin masifar dake tattare da rashin zaman lafiya shi ya fi kowa sani a matsayinsa na kasancewa gwamnan jihar Borno mahaifar 'yan ta'addan Boko Haram. Yace idan yaro yace bai iya gudu ba bai ga abun gudu ba ne. Yace idan matasan arewa basu san ma'anar rashin zaman lafiya ba su nemi wani a jihar Borno yayi masu bayani.

Yace a matsayinsu na kasancewa shugabannin a arewa idan sun ga abun da zai kawo tashin hankali da rashin zaman lafiya dole ne su tsawata saboda banbancinsu ke nan da sauran kasar.

Ga Ibrahim Abdulaziz da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG