Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Trump Na Neman Wanda Zai Nada Shugaban Ma'aikatansa


Mutumin da ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai nada sabon shugaban ma’aikacin ofishinsa, yana shirin barin babban aikinsa a fadar White House.

Rahotanni na cewa Nick Ayers, shugaban ma’aikatan ofishin mataimakin shugaban Mike Pence, yana shirin ajiye aikinsa a karkashin wannan gwamnati a karshen shekara.

Trump ya ce yana neman mutumin da zai yi aiki a fadar White House akalla nan zuwa lokacin yakin neman zaben shekarar 2020.

Yanzu da Ayers ya kaucewa aikin, rahotanni na cewa shugaban kasar na duban yiwuwar bada aiki ga sakataren baitalmalin Steve Mnunchin, ko darektan ofishin kasasfi Mick Mulvaney ko kuma dan ra’ayin mazan jiya dan majalisar Republican Mark Meadow a matsayin sabon shugaban ma’aikata ofishinsa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG