Masu ruwa da tsakin da suka hada da shugabannin tsaro a Najeriya, mataimakiyar shugaban Majalisar Dinkin Duniya da dai sauran su sun jadada mahimmancin hadin kai a yaki da ayyukan ta’adanci da nahiyar Afrika ke fama da su, a yayin bude taron yini biyu da ofishin mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro da hadin gwiwar ofishin yaki da ayyukan ta’adanci na MMD suka shirya a birnin tarayya Abuja.
A yayin taron, gwamna Babagana Umara Zullum na jihar Borno ya ce daukan matakan bai daya, yin sulhu da hadin kan kasashen nahiyar Afrika na da mahimmancin gaske wajen kawo karshen matsaloli masu alaka da ta’adanci a Najeriya da saura sassan nahiyar Afrika.
A cewar mataimakiyar shugaban MDD, Amina J. Muhammad, taron da ya hada shuwagabannin kasashen nahiyar Afrika da dama baya ga wasu jiga-jigai a kasashen duniya, zai taimaka matuka wajen samo bakin zaren matsalar ta’adanci ganin yadda yanzu aka fara bada muhimmanci ga wadanda ayyukan ‘yan ta’adda ya fi shafa wato mata da yara.
A nasa bangare mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ganin yadda bangaren yammancin nahiyar Afrika ya zamo faggen ‘yan ta’adda sanadiyar tara kwararru a fannin tsaro daga kasashen duniya don zama da tattaunawa don a fahimci juna wajen samo mafita mai dorewa.
Masana tsaro da dama sun sha jadada cewa, ta’addanci barazana ce ga zaman lafiya da tsaro a fadin duniya, musamman a Afirka inda aka fi jin tasirinsa.
Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa Najeriya ta shafe sama da shekaru 10 tana fama da ayyukan ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan bindiga da ake kallon sun samo asali ne daga kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar su ISIS da Al-Qaida da masu alaka da su, wadanda a baya sun sami gagarumar nasara a yankin Sahel kuma suna tafiya kudu zuwa mashigin tekun Guinea.
A bangaren kudanci da tsakiyar Afirka, kungiyoyin da ke da alaka da Da'esh na ci gaba da afkawa mutane, musamman a arewacin Mozambik duk da nasarar da aka samu na yaki da ta'addanci a yankin da kuma Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Sai kuma a gabashin nahiyar Afirka inda kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya ta kasance wata barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma, a yayin da Sudan ta kasance wata hanyar jigilar mayakan da ke tafiya zuwa Libya, da yankin kahon Afirka da kuma yankin Sahel.
Masana dai sun ce idan ana son samun nasara a yaki da ta'addanci a nahiyar Afrika ya kamata masu ruwa da tsaki ciki da kungiyoyin yankunan nahiyar Afirka su taka muhimmiyar rawa.
Domin karin bayani saurari rahotan Halima Abdulrauf.
Dandalin Mu Tattauna