Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sandan Jihar Sokoto Sun Kama Mutum Biyu Kan Harin Da Aka Kai Wata Kasuwa


Yan bindiga
Yan bindiga

Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a wani hari da aka kai kasuwar kauye da ya yi sanadin mutuwar mutane shida a Kiri, cikin karamar hukumar Gada ta jihar Sokoto.

WASHINGTON, D. C. - Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Lahadi da gidan talabijin na Channels.

Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka kai hari kasuwar. A cewar Rufa'i, an kama wadanda ake zargin tare da wasu kayayyaki da suka hada da shanu uku da kuma bindigar Dane.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin ‘yan asalin sabon garin Dole ne a karamar hukumar Goronyo ta jihar duk kuma sun amsa laifinsu.

A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan ta ce tana gudanar da bincike kan zargin kashe wani da ake zargin dan fashi da makami ne da wasu ’yan daba suka kashe a titin tsohon filin jirgin sama na jihar.

Majiyoyi a cikin al'ummar sun ce wani harin da aka kai ya kai ga mutuwar wanda ake zargi ‘dan fashi ne da ya kutsa cikin al'ummar tare da wasu mutane biyu wanda a yanzu haka rundunar ‘yan sandan ta ce ta sha alwashin daukar matakan da suka dace bayan kammala bincike.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG