A cikin wata sanarwa da kamfanin na Orano mallakar kasar Faransa ya sanar da sake maka gwamnatin Nijar a gaban kotu bisa dabaibayin da ya ce gwamnatin Nijar ta yi masa a harkar kasuwancin ma’adinan da ya ke hakowa ya jefa mahakar Somair da ke arewacin Nijar a cikin mummunan yanayi na rashin kudi tare da haddasa masa asara mai yawa.
Matakin dai na zuwa ne bayan korar karar da Orano ya shigar kan gwamnatin Nijar a watan Disamban shekarar da ta gabata kan kwace masa lasisin hako Uranuim a mahakar Imouraren.
To sai dai da yake tsokaci Ilyassou Boubakar mamba a kungiyar da ke sa ido kan yadda ake hako ma’adinan karkashin kasa a Nijar na ganin akwai bukatar gwamnatin Nijar ta tanadi kwararrun masana da kuma wadanda za su shigar mata a gaban kotun.
A wannan karon kamfanin ya shigar da karar ne a gaban cibiyar da ke warware sabani da zuba jari da ake kira Cirdi inda ya ke neman a biya shi diyya dai dai da asarar da ya tafka a mahakar Uranuim dake arewacin Nijar.
To a nasu bangare kungiyoyin farar hula a Nijar na ganin kamfanin Orano shi ne ya kamata ya biya diyyar barnar da ya yi wa al’umma na zuba musu guba da ta haddasa musu cuttutuka tsawon shekaru da dama.
Sai dai wasu ‘yan Nijar na ganin abi hanyoyin sulhu domin warware rikicin cikin ruwan sanyi yadda kowane bangare zai amfana.
Kawo yanzu dai gwamnatin Nijar ba tace komai ba game da wannan sabuwar takaddamar da ta kunno kai, sai dai da yawa daga cikin ‘yan Nijar sun zuba ido su ga yadda za ta kaya a gaban kotun tsakanin Orano da gwamnatin kasar yayin da rahotanni ke cewa wannan ita ce hanya daya tilo da ta ragewa Orano domin a bi masa hakkokinsa bayan da ya kasa cimma nasara ta hanyoyin sulhu.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna