Ministan kyautata rayuwar mata da kula da jin dadin jama’a Haj. A’isha Jummai Alhassan ta bayyan haka wa taron fadakarwa wa kungiyoyin mata da ta kira a dakin taron gidan gwamnati dake Yola fadar jiha. Ta ce rancen wanda babu kudin ruwa akansa, an tsara shi don rage talauci da samarwa matan wata kafa da zasu soma kananan sana’o’in kasuwanci.
Hajiya. A’isha ta ce bayaga jihohin Borno da Yobe na arewa maso gabashi kasar, akwai jihohi biyar, daya daga kowane shiyyar Najeriya da zasu anfana daga wannan shirin yaki da talauci wanda aka yi wa lakabin ‘JARIN MATA’ da ake sa ran zasu biya cikin watanni shida.
Wakiliyar asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya Malama Hanatu Yaro da take bada nata gudumawar ta ce shirin zai taimaka wajen rage jefa mata da yara mata hanun wadanda ke anfani da matsin rayuwa da matan ke fama da shi wajen cin zarafi da gallaza masu.
Wata uwar marayu Fatima Isma’il ta bayyana irin tasirin da rancen zai yi wajen bunkasa sana’ar saye-da sayarwa da kananan sana’o’I ta hanyar samar masu sukunin daukar dawaniyar marayu da ke gabansu.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.