Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin Da Talata Ranakun Hutun Bukukuwan Babbar Sallah


Ministan Cikin Gida, Olubunmi Olatunji-Ojo
Ministan Cikin Gida, Olubunmi Olatunji-Ojo

A sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gidan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar a yau Juma'a ya taya al'ummar Musulmi dake ciki da wajen kasar murnar zagayowar wannan lokaci.

Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin 17 da Talata 18 ga watan Yunin da muke ciki su zama ranakun hutun bukukuwan babbar Sallah.

A sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya taya al'ummar Musulmi dake ciki da wajen kasar murnar zagayowar wannan lokaci.

Ministan, a sanarwar, ya jaddada cewar gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta kudiri aniyar tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar 'yan najeriya."

"Ya kuma kara yiwa al'ummar Musulmi da 'yan Najeriya nasihar cigaba da nuna goyon baya da hadin kai ga shugaban kasa a kokarinsa na fadadawa da bunkasa da kuma farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin hanzari."

"A yayin da yake yiwa al'ummar Musulmi fatan yin bukukuwan babbar sallah lafiya, ministan ya shawarci 'yan Najeriya su kudiri aniyar gadarwa 'ya'yansu kasa mai yawar arziki.

Tunda fari, rahoto ya gabata cewar shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Abuja, fadar gwamnatin Najeriya, zuwa Legas a yau Juma'a domin bikin babbar Sallah.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG