Kamfanin dillancin labaran Syria wato SANA, ya bada rahoton cewa, rundunar sojoji ce ta bada sanarwar cewa, an kara wa’adin yarjejeniyar ta Aleppo wacce ta fara aiki a ranar Juma’a zata kuma ta kare yau Talata.
Amurka da Rasha ne suka taimaka wajen kawo yarjejeniyar tsagaita wuta a garin, kwatankwacin wacce aka samar a garuruwan Latakia da gabashin Ghouta a watan da ya gabata.
A matayin wani bangare na tabbatar da dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta a duk fadin kasar da aka cimma a watan Fabrairun da ya gabata. Aleppo na daya daga wuraren da aka tafka mummunan fada a ‘yan makonnin baya-bayan nan.
Wanda daga watan Afirilun bana zuwa ‘yanzu aka hallaka farar hula kusan 300, abin da ya hada da hari da sama da harin da aka kai kan asibitocin garin. Amurka tace cimma kananan tsagaita wuta na da muhimmanci akan ‘yarjejeniyar tsagaita wuta a fadin kasar.