Wani sabon rahoto da hukumar kare ‘yancin bil Adama ta Sudan ta Kudu ta fitar na cewa ma’aikatan tsaron kasa na ci gaba yiwa mata da ‘yan mata fyade, da kuma kama mutane da ‘daure su babu gaira ba dalili a fadin kasar.
Rahoton mai shafi 53 da aka fitar jiya Laraba, ya kuma bayyana cewa yawancin mutanen da ake ciwa zarafin basu da hanyar samun yadda za a bi musu kadin wannan cin zarafi.
Rahoton ya bayyana cin zarafin mutane da kuma kisan kare dangi da jami’an tsaro suka yi cikin shekaru biyu da suka gabata.
Masu suka sunce dole ne hukumar ta ‘dauki matakin da ya wuce hada rahoto, ya kamata ta ci gaba da kula da bibiyar take hakkin bil adama ta kuma tabbatar da ganin cewa an kama duk wanda ya aikata hakan.
Facebook Forum