Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce an kawo karshen matsalar barkewar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera, da ta hallaka mutane 400 a kasar.
Hukumar ta lafiya tare da hadin kan jami’an ma’aikatar lafiyar kasar ta Sudan ta Kudu ne suka bayyana kawo karshen cutar a wani taron manema labarai da aka yi a Juba.
Barkewar cutar, wacce ita ce mafi girma a tarihin kasar, ta faro ne daga tsakiyar shekara 2016 a daidai lokacin da sabon fada ya barke a Juba.
Ministan kiwon lafiya a kasar ta Sudan ta Kudu, Riek Gai Kok, ya ce, cikin makwanni bakwai da suka gabata, ba a sake samun wani da ya kamu da cutar ba a duk fadin kasar, amma ya ce, hakan ba ya nufin mutane su yi sakaci bane.
Facebook Forum