Tallafin man fetur din da ya kai nera miliyan dubu daya baya cikin kasafin kudin shekarar 2016.
Karamin ministan man fetur Ibe Kachikwu ne ya bayyana hakan. Kudin tallafin ne yake sa dillalan man jan kafa wajen kawo mai matuka gwamnati bata saki kudin ba.
Ibe Kachikwu yace ya zama wajibi matatun man fetur na cikin gida su fara aiki ko menene ma za'a yi. Yakamata a dinga tace man a cikin gida ba a dogara da kawoshi daga kasashen waje ba.
Karamin ministan ya zagaya ya duba matatar man dake Kaduna wadda ke gabanin soma aiki bayan bayana fara aikin matatun man dake Fatakwal. Ministan yace zasu sanya hannu da kwararrun duniya akan lamuran mai su shigo su tallafawa kasar domin raya matatun man.
Shirin ya nuna duk dillalen man fetur ka iya shigo da man ba tare da rage farashin ba domin amsar tallafi daga gwamnatin tarayya. Kachikwu yace lita a hukumance zata cigaba da kasancewa kan nera 87 kafin ta ragu ko ta fi haka a farkon shekarar 2016.
Ministan bai yi bayanin rage nera biyu ba akan litar man da kafofin labaru suka yayata. To saidai tuni man fetur ya fara wadata a birnin Abuja fadar gwamnatin tarayya akan farashin nera 87 kowacce lita amma da alamun wasu gidajen man kan birkita inji yadda mota kan sha man da bata saba zuka ba.
Ga karin bayani.