Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Haramta Sana’ar Canjin Kudi a Najeriya Sai Da Rijista


Naira, Takardun Kudin Tarayyar Najeriya
Naira, Takardun Kudin Tarayyar Najeriya

Babban bankin Najeriya CBN, ya sanar da haramtawa ‘yan canjin da bas u da rijista yin wannan sana’a ta canjin kudaden na kasashen waje nan da sabuwar shekarar da za a shiga.

Sanin kowa ne sana’ar canjin kudin kasashen waje na daya daga hada-hadar da jama’a suka yiwa kamun kazar kuku a Najeriya. Ta inda kafin kaga mutane sun je banki neman canjin kudi sai ya zama ba yadda zasu yi, don suna ganin ya fi riba.

Kwatsam sai ga sanarwa ta fito daga babban bankin Najeriya na CBN cewa, duk wani dan canjin kudin da bas hi da rijista da gwamnati, wannan sana’a ta haramta gare shi. Tsarin da babban bankin ke ganin yana cikin yunkurin ceton darajar Naira.

Baya ga ‘yan canji masu rijista, akwai dubban mutane da ke reto a ofisoshi da shagunan ‘yan canji suna wannan harkar, hasali ma dai it ace babbar sana’ar da suke ci suke sha kamar yadda wani dan canji ya bayyanawa wakilinmu Lamido Abubakar Sakkwato.

Ga dukkan alamu ‘yan canjin bas u yi maraba da wannan garambawul na CBN ba, domin a ganinsu suna saukakawa mutane wajen samun canjin kudin waje ba tare da wahala ba.

Sai dai shima mai magana da yawun babban bankin Ibrahim Mu’azu ya fayyace wadanda ake nufi da wannan doka. Inda yace akwai halattacciya da kuma haramtacciyar hanyar yin wannan sana’a ta canjin kudi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG