Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekara ta dubu biyu da goma sha shida na Naira triliyon shida da ya kasance kasafin kudi mafi tsoka da gwamnati ta taba gabatarwa.
Da yake gabatar da jawabin shugaba Buhari yace, zasu bi sau da kafa su kuma kwato duk abinda yake alhakin talakawa ko da ina aka boyeshi.
Manyan ayyuka ya sami naira triliyon daya da digo takwas, wanda shine kasha talatin cikin dari na kasafin kudin. Bangaren lafiya ya sami naira biliyan dari biyu da ashirin da daya da digo bakwai, ilimi Naira biliyan dari biyu da ashirin da daya da digo bakwai. Ilimi ya sami Naira biliyan dari uku da sittin da tara da digo shida. Ayyukan cikin gida biliyan tamanin da tara, sufuri naira biliyan dari biyu da biyu, tsaro naira biliyan dari biyu da casa’in da hudu, yayinda kananan ayyuka suka sami naira triliyon biyu da digo sittin da biyar.
A halin yanzu dai shugaba Muhammadu Buhari yace za a bar man farashin man fetir a kan naira tamanin da bakwai lita daya a cikin gida Najeriya.
Wadansu ‘yan majalisa da Sashen Hausa ya yi hira da su sun bayyana kasafin kudin a matsayin, kasafin kudin ceto talakawa da yace ya nuna shugaban kasa ya maida hankali kan inganta rayuwar talaka.
Bisa ga cewarsu, zuwan shugaban kasar majalisa ya gabatar da kasafin kudin da kansa ya nuna yadda ya dauki aikin da muhimmanci.
An dai shirya kasafin kudin ne a kan kudin gangar danyen mai fetir dalar Amurka 38, sannan canjin naira a kan Naira dari da sittin kowacce dala.
Ga cikakken rahoton da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda ta aiko mana daga Abuja.