To amma daga daya ga watan Janairu na shekara mai zuwa babban bankin Najeriya zai dakatar da tsarin.
Mr. Moses Tule daraktan manufofin kudi na babban bankin Najeriya ya bayyana dalilin wannnan sabuwar manufar ta gwamnati. Yace sun yi la'akari da irin badakalar da ake tafkawa da katunan, badakala sosai ba ma zamba cikin aminci kadai ba. Yace kasa na cikin matsalar tattalin arziki wasu kuma suna tallafawa wasu wajen ruguzar da kasar. Yace suna ganin lamarin a matsayin wani kokari ne na yiwa tattalin arzikin kasar ta'arnaki ne.
Akan lokacin da wannan sabuwar manufar zata kare sai Mr Tule yace kowace manufar gwamnati bayan wani lokaci akan yi waiwaye a duba yadda ta kaya. Idan akwai bukatar a yi mata kwaskwarima ko kawar da ita sai a yi.
Amma tuni 'yan Najeriya dake kasashen waje suka fara fargaba da wannan sabon tsarin.Bakari Alhaji Bello Arabi wani dailibi dan Najeriya dake karatu a turai yace mataki ne wanda zai takurawa wadanda suke kasashen waje musamman dalibai. Yace basu da wata hanyar da zasu samu kudin shigowa na biyan bukatunsu. Yau idan aka ce an dakatar da yin anfani da katunan da yawa cikinsu zasu shiga cikin halin kakanikayi. Ya kira gwamnatin Najeriya ta sake yin nazari akan wannan sabuwar manufar.
Ga karin bayani.