Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Juya Injunan Motoci Zuwa Masu Amfani Da Iskar Gas


CNG
CNG

Shirin fadar shugaban kasa na maida ababen hawa zuwa masu amfani da iskar gas samfurin CNG ya soma aiki da rabon kayayyakin sauya injunan motoci zuwa masu amfani da gas guda dubu (1000) a wasu jihohin Najeriya domin rage tasirin radadin janye tallafin man fetur.

A jawabinsa yayin kaddamar da fara rabon kayayyakin aikin sauya injunan motoci zuwa masu amfani da iskar gas a wasu daga cikin jihohin kasar, darakta mai kula da shirin, Micheal Oluwagbemi, yace matakin zai rage tsadar sufuri.

A cewarsa, matakin zai samar da guraben aikin yi na kai tsaye guda dubu 100 a cikin shekaru 3 masu zuwa, inda yake nufin sauya injunan ababen hawa kimanin miliyan 3 cikin wannan wa’adi.

Oluwagbemi ya bayyana cewa za a sauya injunan motocin haya zuwa masu amfani da gas din CNG kyauta domin rage radaden janye tallafin man fetur kuma hakan zai taimaka wajen rage tsadar harkokin sufuri.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG