Sashen Hausa na Muryar Amuka ya tuntubi Darektan hulda da jama’a na hukumar, Yakubu Datti akan wannan batu.
“Mun sha yi musu magana cewa su biya, basu biya basusukan da ake bin su ba. Kuma mu ayyukan da muka a Airport, ba da kudaden gwamnati muke biyan albashi ba. Shi shugaban FAAN Alhaji Saleh Ciroma ya bada umarni cewa an bada nan da kwana bakwai su yi kokari su zo su biya kudaden da suke bin bashi.”
Ya kara da cewa “basusukan dai sun kai kusan Nera biliyan 17, an bada lokaci, an gana da su, amma ba su biya wadannan basusukan ba.”
Sashen Hausa na Muryar Amurka ya bincike matakin da FAAN zata dauka akan duk kamfanin da ya gaza biyan kudaden da ake bin shi.
“Akwai mataki iri-iri, amma ba za mu iya fada ba, sai kamfani ya zauna an yi shawara, za’a san matakin da za’a dauka” a cewar Mr. Datti.
To ko me yasa sai yanzu hukumar FAAN take daukar mataki?
“Ai mun dade muna tayar da maganan biyan basusuka. Akwai lokacin da har mun hana wadansu harka.”