Idan ba'a manta ba hukumar zaben kasar Najeriya wato INEC ta sa watan Augusta mai zuwa lokacin da za'a fara yakin neman zabe gadan gadan. Abun da ya faru a Gulu lokacin kaddamar da sabon asibitin alama ce ta yin watsi da dokar hukumar zaben. Hargitsin 'yan bangan siyasa dake dauke da hotunan magoya bayansu ya kusa tsayar da jawaban da ake yi a wurin kaddamar da asibitin.
Dr Babangida Muazu Aliyu gwamnan jihar Neja yace ya fadawa sakataren jam'iyyarsa da su yi hatara domin hukumar zabe na kallon duk abun dake faruwa kuma zata iya yin hukumci. Shi ma tsohon shugaban Najeriya Janaral Abdulsalami Abubakar dake wurin bikin ya yi anfani da damar da ya samu ya janyo hankalin 'yan siyasa kan muhimmancin zaman lafiya. Yace idan babu zaman lafiya asibitin ba za'a iya samarda shi ba. Sabili da haka ya kira 'yan siyasa su yi hatara su tabbatar da zaman lafiya ganin yadda zaben 2015 ke gabatowa.
Asibitin mai gadajen kwanciya dari da goma an sa masa sunan Janaral Abdulsalami Abubakar. Gwamnatin jihar tace ta kashe nera miliyan 923 wajen ginashi.
Ga rahoto.