Dr. Muhammad Usman, darekta ne a matakin farko, a ma’aikatar lafiya a jihar Neja, yayi bayanin irin mutanen da wannan cuta ke saurin kamawa.
“Da farko mutum ya kasance mace, maza ma sukan samu, amma mata sunfi samun hatsarin wannan cuta. Na biyu macen da bata taba shayarwa ba, ko bata taba haihuwa ba. Sannan tsufa, ba’ace mata kanana baza su iya kamuwa ba. Mata masu jiki, da masu shan taba”, a cewar Dr. Usman.
Madam Aisha Muhammadu Wushishi, bayan kasancewa uwa, kuma jami’ar kiwon lafiya ce a jihar Neja.
“Wata wadda bata sani ba, baza ta san cewa yau tana da ciwon ba. Amma idan taje asibiti tace kamar tana jin wani abu da bai kamata ba, za’a duba ta, a ce mata ko shine, ko ba shi bane.
An raba na’u’rorin gwada cutar sankaron mama guda dubu hamsin da biyar kyauta ga jama’a, a kananan hukumomi ashirin da biyar dake fadin jihar Neja.
Za’a dauki dogon lokaci ana fadakarwa game da wannan cuta ta sankaron mama, a jihar Neja.