A baya gwamnatin ta sha wargaza masu ginan kwarandar a wuraren da suka yi sansani ba tare da samun izini ba domin tsoron gurbata wuri da kuma barkewar cututuka da hakan ke janyowa.
Kwamishanan kula da harkokin ma'adanai na jihar Alhaji Abubakar Jibril ya kira taron manema labarai kan al'amarin. Ya ce laifin bana gwamnatin jiha ba ne. Laifin na gwamnatin tarayya ne. Ya ce gwamnatin tarayya ke bada takardar izinin hako ma'adanai ba tare da sa gwamnatin jiha cikin lamarin ba. Idan mutum ya je Abuja ya ce yana neman izinin ya hako ma'adanai a wata gona sai a bashi. Shi kuma idan ya dawo sai ya ba mai gonar ko nera dubu goma. Yanzu haka suna da irin wadannan matsalolin fiye da hamsin.
Kodayake jiha ba zata iya dakatar da mahakan ba amma tana iya hanasu bata yanayi da ramuka. Dr Ibrahim Tin kwararre kan lafiyar dan adam kuma sakataren ma'akatar ma'adanai ya bayyana illar hakan ma'adanan ba kan ka'ida ba. Ya yi misali da abun da ya faru a jihar Zamfara wanda ya hallaka yara da dama ya kuma nakasa wasu har iyakacin rayuwarsu. Wasu sinadarai daga abubuwan da ake hakowa idan ba'a bi kaida ba sukan taru su gurbata mafitsarin mutum gaba daya. Kwakwalwa ma ta kan tabu. Idan yaro ya kamu ko ya girma ba zai iya ma karatu ba.
To sai dai kamfanonin hakan ma'adanai a jihar sun ce basu cikin irin hadarin da a ke tunane. Alhaji Danlami Sarkin Daji daya daga cikin masu hakan ma'adanai ya ce su basa anfani da guba mai cutarwa irin wadda mutanen Zamfara suka yi anfani da ita lokacin da a ka hana fashin dutse.
Ga karin bayani.