Sabili da cecekucen da suka taso kan dokar gwamnatin jihar Neja ta yi karin haske game da matakin da ta dauka na hana sana'ar kabu-kabu a Minna. Kwamishanan harkokin sufuri Alhaji Garba Mohammed ya shaidawa Muryar Amurka cewa dokar na nan daram.
Kwamishanan ya ce hakin gwamnati ne ta kare rayukan jama'a kuma ana anfani da babura ana kashe mutane. Ya ce idan an kashe mutane goma tara daga 'yan kabu-kabu ne. Idan kuma an harbe mutum ko kuma an karye duka za'a gani lamarin daga 'yan achaba ko kabu-kabu ne. Mutane na kama sana'ar achaba ba tare da samun wani horo ba. Dalilan ke nan da ya sa gwamnati ta dauki wannan matakin. Ba'a yi dokar domin a muzgunawa jama'a ba.
Jiya da dokar ta fara garin ya samu lafiya. Sufuri na tafiya tsaf. Babu wani hargitsi kaman da. Da 'yan achaba idan suka aikata wani laifi sai su gudu. Dangane da cewa jama'a da 'yan majalisu na tarayya da na jiha sun bukaci gwamnati ta sassauta dokar har sai an samu isasshen ababen hawa kwamishanan ya ce sun ji koken kuma sun yi ma mutane adalci. Ya ce sun kwashe fiye da shekara daya sun bada sanarwa zasu yi dokar.Su 'yan achaban suka ce kafin a soma a samu keke napep dubu daya. Ya ce sun samardasu guda dubu dayan.
Ga karin bayani.