Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Rushe Gidan Rediyon Breeze FM


Tilas ne a nemi izin daga hukumar raya biranai kafin a aiwatar da gini domin bin dokar da Gwamnati ta shinfida

Hukumar gidan Rediyon Breeze FM wanda gwamnatin jihar Nasarawa ta rushe tace ta shirya tsaf, na kai gwamnatin gaban kuliya.

A taron manema labarai da darektocin gidan Rediyon suka kira sun bayyana cewa gwamnatin jihar Nasarawa, bata bi matakan da suka dace wajen rushe gidan Rediyon ba.

Mr. Nawani Aboki, shine ya mallaki gidan Rediyon na Breeze FM, yace jama’ar jihar Nasarawa, sunce dole a kai Gwamnan jihar kotu. Ya kara da cewa hukumomin jihar sun tuhumesu cewa yaya suka kafar gidan Rediyon babu izini aka kuma bukacesu da su nemi izini suka kai takardan neman izini ranar juma’a da safe jami’an suka ce suna yajin aiki sai suka koma da yamma sai aka lika takardan rushe gini da safiyar asabar saisuka aiwatar da rushe ginin.

A bangaren gwamnati kuwa kwamishinan yada labarai da raya al’adu a jihar ta Nasarawa, Abdulhamidu Yakubu Kwara, yace takardan mallakar fili da aka baiwa mai gidan Rediyon domin ya gina gidan zama ne ba gidan Rediyo ba kuma idan har yana bukatar gina gidan Rediyo sai ya nemi izini yin haka kuma gwamnati ta tabbatar masa da ita.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG