Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Sace Yara Da Aka Yi a Jami'ar Greenfield


Kwana guda da sake sace dalibai a jahar Kaduna, gwamnatin jahar ta ce har yanzu ba wani labari game da adadin daliban da aka sace ko kuma inda aka boye su. 

A daren Talata ne dai wasu 'yan-bindiga su ka shiga Jami'ar Greenfield da Kaduna inda su ka kashe wani ma'aikacin Jami'ar sannan su ka sace dalibai da dama.

Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna Mal. Samuel Aruwan ya ce har yanzu ba a tantance adadin daliban da aka sace ba amma jami'an tsaro sun dukufa wajen ceto daliban da aka tafi da su.

Ita dai gwamnatin jahar Kaduna ta dage kan cewa ta na iya nata kokari don dakile matsalar tsaro, inji Kwamishinan tsaron jahar Malam Samuel Aruwan.

Wannan harin satar daliban Jami'ar dai na zuwa ne a daidai lokacin da iyayen daliban kwalejin gandun daji da ke Mando ke cigaba da kokawa game da dadewar 'ya'yan su a hannun yan-bindigan da su ka sace su.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG