Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon rikicin Tuta a Jihar Carolina Ta Kudu


Membobin Ku Klux Klan
Membobin Ku Klux Klan

Fada ya barke a wajen zanga-zanga a jihar Kudanci Carolina tsakanin ‘yan tawagar KU KLUX KLAN masu fushin da sauke tutar nan ta Confederal dake tsakiyar birnin.

Inda suka suka yi gaba da gaba da ‘yan fafutukar bakaken fatar Amurka da suke tasu zanga zangar a daya gefen. Yan sanda a birnin sun cafke mutane da dama game da lamarin.

Hukumomi sun ce ‘yan fafutukar sun taru ne don bayyana matsalar kabilancin da suke fama da ita a jihar. James Evans Muhammad ne ya jagoranci zanga-zangar.

‘Yan sanda sun tarwatsa jama’ar. Shugaban Amurka Obama tuni ya kira cire tutar da cewa mataki ne na ‘yan majalisar jihar akan kyakkyawan yunkurin magance wariyar launin fata.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG