Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Borno Ta Tallafawa Wadanda Rikicin Boko Haram Ya Kwantar a Asibitoci


Wasu da suke kwance a asibiti
Wasu da suke kwance a asibiti
Cikin jihohi uku a arewa maso gabas dake cikin dokar ta baci sanadiyar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke yawan kaiwa, jihar Borno ita ce ta fi kowace jihar da aka fi kaiwa hare-hare dare da rana. Ita ce kuma tafi asarar jama'a da dukiyoyi da yawan wadanda suka rasa muhallansu.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda ya yi fira da Alhaji Bulama Guyo shugaban kwamitin tallafawa wadanda suka jikata sanadiyar hare-haren kungiyar Boko Haram. Makon da ya gabata sun zagaya anguwanni da ma wasu kauyuka sun bada taimako musamman ga wadanda suka rasa abinci da muhallansu. Bayan haka kwamitin ya zagaya asibitoci domin tallafawa wadanda rikicin ya kwantar dasu a asibitoci.

Alhaji Guyo yace duk wadanda suka jikata sanadiyar hare-haren Boko Haram dake kwance a asibiti sun je sun gansu. A asibitin koyaswa sun samu mutane saba'in kana sun ba kowane mutum nera dubu goma goma domin su samu su sayi wasu kayan da suke bukata. Ban da haka gwamnati ce zata biya kudaden magungunansu da kudaden da asibiti zata nema a biya. Duk wanda rikicin Boko Haram ya kai asibiti gwamnati ce ta dauki nauyinsa. Haka ma kwamitin yayi a asibitin cikin gari inda mutane talatin ke kwance. A asibitin Umaru Shehu yaro daya ne ke kwance a asibitin wanda ya samu mummunan kuna yayin da ya tsere daga dakinsu inda 'yan Boko Haram suka yanka 'yanuwansa kamar raguna.

Daga karshe dai sun samu sun je asibitoci hudu har da na 'yansanda musamman batun 'yansanda biyar da 'yan kunan bakin wake suka rutsa dasu. Kwamitin ya ziyarci iyalan 'yansandan ya bayarda gudunmawar nera dubu dari biyar da kayan abinci kafin gwamnan ya dawo.

Ga karin bayani
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG