Duk da rasa jami'an kwamisahanan 'yansandan yace rundunarsa ba zata gaji ba ko ta karaya a kokakrinta na kare lafiyar jama'a da dukiyoyinsu a duk fadin jihar. Kwamishanan ya yi furucin ne lokacin da ya ziyarci inda aka samu asarar rayukan wasu jami'an 'yansanda guda biyar.
Wanan lamarin ya faru ne yayin da 'yansandan suka bi wata mota kirar golf da mutane uku cikinta. Sun tsayar da motar domin su binciketa amma ta ki tsayawa dalilin da ya sa suka bita. Suna gap da cimma motar sai mutanen dake cikin motar suka tayarda bam dake cikin motar. Lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutanen uku dake cikin motar da 'yansandan guda biyar dake binsu a cikin tasu motar. Lamarin ya faru ne da misalin karfe tara da rabi safiyar jiya a kan titin Dalori kan hanyarsu ta shiga Maiduguri.
Ana zaton maharan ko kuma 'yan kunar bakin waken sun fito ne daga dajin Sambisa da nufiN kai hari cikin birnin Maiduguri. Kwamishanan 'yansandan Lawal Tanko yace mutanen suna kokarin shiga Maiduguri ne amma mutanenSA da suka yi kokarin hanasu sun biya da rayukansu.
Bayan tashin wannan bam ne aka sake jin tashin wani a kauyen Amarwa dake karamar hukumar Konduga. A nan ma wani ne a cikin motar girar golf ya kutsa cikin mutane kana ya tada bam da ya kashe mutane uku ya kuma raunata wasu su goma sha biyar. Daya daga cikin wadanda abun ya shafa dake kwance a asibitin koyaswa na Maiduguri ya bayyana yadda lamarin ya faru.
Ana zaton maharan na kokarin shiga da bama bamai cikin birnin Maiduguri ne lamarin da ya sa "Civilian JTF"suka tsaurara binciken ababen hawa.
Ga karin bayani.