A wani bincike da gwamnatin jihar Sokoto, ta gudanar da hadin guiwar wani kamfanin kasar China, tace an gano ma’adanin Coal, mai yawa dake jiran a hako domin samarda makamashi da kuma habaka tattalin arzikin jihar dama na kasa baki daya.
Wata sanarwa da kakakin Gwamna jihar Imam Imam ya fitar tace tuni da kafanin Siminti, na arewa dake Sokoto, ya kudiri aniyyar amfani da ma’adanin na Coal, domin samarda makamashin mai karfin Mega Watts 40, da ake dasawa a kamfanin.
Ma’adanin na Coal, kari ne ga kusa ma’adanai 20, da bincike ya gano a jihar ta Sakoto, da suka hada da zinari da kwallin kura da bakin karfe da kuma sinadarin yin takin zamani da sauransu.
Kwamishinan ma’adanai da albarkatun kasa na jihar Sokoto, Bello Muhammad Gwaranyo, yace kafa kamfanoni a jihar domin cin gajiyar wadannan albarkatun kasa zai taimaka wajan samarda aikin yi ga matyasa.
Wani al’amari dake ciwa gwamnatoci jihohi tuwo a kwarya shine yadda gwamnatin tarayya dake maidasu saniyar ware wajan hakopwa da amfana da albarkatun kasa wanda ake zargin baya samun kulawar da ta kamata.