Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Syria Tayi Asarar Wani Sansanin Sojojinta


'Yan tawaye suna murnar nasarar da suka samu
'Yan tawaye suna murnar nasarar da suka samu

'Yan tawayen Syria sun cafke wani sansanin sojojin Syria.

A jiya talata wani matsakaicin rundunar yan tawaye a Syria ya samu nasarar kwace daya daga cikin sansanin sojoji gwamnatin kasar.

Rundanar ta hadin gwiwa ta samu nasarar karbe bataliya ta 52, wadda mai Magana da yawun rundunar yan tawayen yace fada ne da aka yi cikin dan kankanin lokaci amma kuma cike da tasiri.

Kungiyar nan mai kare hakkin bil adama dake da hedikwata a Ingika mai suna SYRIAN OBSERVATORY FOR HUMAN RIGHT ta bayyana cewa sojojin gwamnati 20 ne aka kashe kana nayan tawaye 14.

Su dai wadannan sojojin suna kusa ne da babban titin zuwa Damasscuss wanda yake daura da bakin iyakar Jordan da Syria a cikin lardin Daraa.

Sojojin Syria dai sun samu mummunar koma baya a cikin yan watannin nan ciki ko har da rasa ikon bakin iyakar su da Jordan zuwa hannun yan tawayen.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG