Bisa ga umurnin gwamnatin tarayya jihar Gombe ta tanadi wurin da zata tsugunar da 'yan gudun hijira fiye da dubu ashirin da suke tsugune a kasar Kamaru.
Babban sakatare na hukumar samarda agajin gaggawa Dr. Danlami Araf Lukuje yace gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnatin jihar ta tanada mata wurin da zata zaunar da 'yan gudun hijira 'yan kasar da tashin hankali da wasu abubuwa suka sa suka tsere zuwa Kamaru.
Aikin kafa sansanin da tsugunarda 'yan gudun hijirar na gwamnatin tarayya ne. Yace abun da suka sani gwamnatin tarayya ta tunkari jihar Gombe domin ta taimaka wurin karbar 'yan Najeriya da zasu dawo gida. Gwamnan jihar kuma ya amince da bukatar. Wasu sun fito ne daga Afirka Ta Tsakiya, akwai kuma 'yan Najeriya da rikicin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa suka tilast masu suka tsallake iyaka suka shiga Kamaru.
Kafin wadanda zasu zo yanzu da can jihar Gombe tana da 'yan gudun hijira kusan mutane dubu goma da suka fito daga Yobe da Borno. Su ba'a sansani aka ajiyesu ba.
A wuraren da jihar Gombe ke kula da masu gudun hijira wakilin Muryar Amurka Abdullwahab Muhammed ya samu ya zanta da wasu. Wata da ta fito daga Afirka Ta Tsakiya tace fitinar kasar ce ta sa suka gudo. Sun bi ta Chadi kafin su shiga Kamaru. Tace dama Gombe garin mahaifinsu ne. Ya taso ya koma Gombe su kuma suka cigaba da zama Afirka ta Tsakiya. Shi ma Abubakar Ahmadu daga Afirka Ta Tsakiya ya fito. Yace suna cikin makaranta aka fada masu ana yanka mutane sai suka gudu ba tare da daukan komi ba. Akwai wasu kuma daga Damboa wadanda suka ce ana taimaka masu da abinci.
Ga rahoton Abdullwahab Muhammed.