Dr Bawa Abdullahi Wase kwararre akan harkokin tsaro yace akwai abun dubawa game da taimakon da Amurka tace zata baiwa Najeriya domin kubuto daliban Cibok da 'yan Boko Haram suka sace. Yace ga Amurka faduwa ce ta zo daidai da zama domin dama tana da burin mamaya ta kafa sansanoni yadda idan zata kai farmaki zata samu da sauki. Idan kuma ta kama za'a yi rabon gadon dukiya ne to a yi da ita.
Dr Wase yace taimakon ya tabbatar da take-taken kasar Amurka. Yace dama tashin tashinar da ake gani da irin motocin da 'yan ta'adan ke anfani da su alamu ne dake nuna cewa akwai hadin bakin kasashen waje.
Shi ma Manjo Shinko mai murabus yace koda Amurkawan sun shigo muddin ba'a hau teburin sulhu ba kwaliya ba zata biya kudin sabulu ba. Yace sojojin Najeriya basu da rauni wurin da 'yan ta'adan suke shi ne yake da wuya. Ko su Amurkawan idan sun zo zai basu wuya. Abu na biyu su 'yan ta'adan ba kayan yaki suke sawa ba, a'a suna sa kayan fararen hula ne domin haka lamarin nada wuya. Abu na uku 'yan ta'adan yakin sunkuru su keyi. Sabili da haka zai yi wuya Amurkawan su samu yadda suke tsammani. Ko a Afghanistan Amurkawan sun nemi a yi sulhu.
Manjo Shinko ya kara da cewa Amurkawa zasu yi anfani da daman ne su samu su shigo, idan sun shigo kuma babu maganar fita. A cewarsa " abun nema ya samu tunda dama suna neman wurin zama ne"
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.