Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Amince Da Yadda Ake Takurawa Kananan Hukumomi Ba – Kungiyar Kwadago NLC


ABUJA: 'Yan kungiyar kwadago masu zanga zanga
ABUJA: 'Yan kungiyar kwadago masu zanga zanga

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC tace ba za ta amince da yadda gwamnatoci jihohi ke ci gaba da takura ‘yancin kananan hukumomi ba, kasancewa suma hukumomi ne masu zaman kansu bisa kundin tsarin mulkin kasar.

Da yake nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda gwamnatocin jihohi a Najeriya ke yiwa kananan hukumomi kama karya, shuagaban kungiyar NLC, Kwamarad Ayuba Wabba, ya ce ba zasu amince da hakan ba.

Ganin yadda gwamnoni ke takurawa kananan hukumomi har ta kai ga wasu lokuta ba a gudanar da zabe sai dai a nada Kantomomi, kuma kudade basa zuwa kai tsaye da kananan hukumomi, hakan yasa basa iya yin aikin komai. A cewar Kwamarad Ayuba.

A cewar wani tsohon shugaban karamar hukuma Kwamrad Aminu Abdussalam Gwarzo, na cewa an sami matsala ne tun farko bisa yadda ‘yan Majalisun jihohi suka zama tamkar ‘yan amshin Shata a hannun gwamnatocin jihohinsu.

Kananan hukumomi dai na da matukar muhimmanci ganin cewa sune matakin farko da ‘yan kasa zasu iya kai kukansu.

A baya-bayan nan ne kwamitin da gwamnatin APC ta kafa kan gyaran tsarin mulkin Najeriya, karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i ya bada shawarar a soke tsarin kananan hukumomi gaba daya.

Domin karin bayani saurari rahotan Hasssan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG