Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Gargadi 'Yan Kasar Su Kasance Masu Bin Doka


 Janar Abdulrahaman Dambazau, Ministan Harkokin cikin Gidan Najeriya
Janar Abdulrahaman Dambazau, Ministan Harkokin cikin Gidan Najeriya

Biyo bayan yamutsin da ya faru a Jos babban birnin jihar Filato tsakanin 'yan kabilar Igbo da wasu, Janar Abdulrahaman Dambazau ministan harkokin cikin gidan Najeriya ya kai ziyarar gani da ido inda ya gargadi ilahirin 'yan Najeriya da su kasance masu bin doka

A madadin gwamnatin Najeriya ministan harkokin cikin gida Janar Abdulrahaman Danbazau ya gargadi 'yan Najeriya da su kasance masu bin doka.

Ministan ya fada haka ne yayinda ya kai ziyarar gani da ido zuwa Jos babban birnin jihar Filato inda rikicin bangaranci ya barke jiya.

Ministan ya gana da shugabannin al'umma da na addinai da kabilu daban daban ya kuma yiwa Muryar Amurka bayaninsa dalilinsa na zuwa jihar Filato.

Yana mai cewa "Mun zo Filato don mu gani kuma mu ji a kan abubuwan da suka faru, domin mun ji labarin an dan samu tashin hankali sanadiyar abun da ya faru a kudu maso gabas; cewa an yi kashe kashe da kone kone saboda haka mutane a nan suka nemi yadda zasu dau fansa. Allah da ikonsa da mai girma gwamna kuma da jami'an tsaro a wannan jiha sun tashi tsaye sun kashe wutar".

A kan matakan da gwamnati zata dauka domin dakile tashin hankali a duk fadin Najeriya, ministan yace mataki na daya shi ne bin doka. A cewarsa " duk wanda yake dan Najeriya ne ya san da doka a ksar; ya san kuma da gwamnati. Gwamnatin nan hakki ne a kanta ta tabbatar ta kare mutuncin jama'a da dukiyoyinsu".

Kakakin kungiyar Jama'atul Nasril Islam, JNI, reshen jihar Filato Malam Sani Mudi yace sun dauki matakan dakile duk wani tashin hankali a cikin jihar Filato. Yace sun tashi tun jiya suna kwantar da hankulan mutane musamman matasa domin su ne suka fi harzuka. Yace an ci nasarar shawo kan lamarin kuma ana hada kai da gwamnati da jami'an tsaro.

Shugaban raya al'adun gargajiya na kabilar Igbo a birnin Jos Hycient Samuel yace basu ji dadin faruwar lamarin ba. Yace sun kira mutanensu sun fada masu babu ruwansu da masu rajin neman kafa kasar Biafra. Duk wanda yake son kafa Biafra ya tattara kayansa ya koma kudu maso gabashin kasar. Mutanensu biyu sun rasa ransu a yamutsin na jiya wasu da dama kuma sun jikata.

Gwamnan jihar Simon Lalung yace zasu cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki har sai an samu mafita.Yana mai cewa idan da basu dauki matakan da suka dauka jiya ba, da yanzu ba za'a san inda ake ba.

Kawo yanzu dai zirga zirgan jama'a ta ragu cikin tsakiyar birnin yayinda shaguna da dama suka kasance a rufe. Jami'an tsaro kuma na cigaba da aikinsu.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG