Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 - Dalibai Na Shirin Komawa Azuzuwa A New York


Dalibai
Dalibai

Adadin kamuwa da cutar COID-19 a fadin duniya na ci gaba da karuwa, inda ya haura sama da miliyan 19 da dubu dari daya, a cewar jami’ar John Hopkins.

Har iyau Amurka ce a kan gaba wurin yawan kamuwa da cutar da mutum miiiyan hudu da dubu dari tara, kana kasar Brazil na biye da ita da mutum miliyan biyu da dubu dari tara sannan India na matsayi na uku da mutum miliyan biyu na wadanda suka kamu da COVID-19.

Gwamnan jihar New York Andrew Cuomo ya fada a jiya Juma’a cewa zai baiwa dalibai daman komawa azuzuwa a jihar a farkon shekarar karatu saboda nasarori da aka samu wurin dakile coronavirus.

Shwarar Cuomo zata baiwa dalibai daman shiga azuzu yayin da suke saye da takunkumin rufe baki da hanci, haka zalika zasu iya daukar karatu ta yanar gizo a inda suke.

Manyan garuruwan Amurka kamar Chicago da Houston da Los Angeles da kuma Miami suna cikin inda dalibai zasu fara shekarar karatu yayin da suke daukar karatu ta yanar gizo a wuraren da suke.

An dakatar da akalla wani dalibi guda na wata makarantar sakandare a jihar Georgia dake kudancin Amurka, wanda ya kafe hoton harabar makaranta cike da mutane a yanar gizo, yana nuna dimbin dalibai ba tare da abin rufe baki da hanci ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG