Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Kano Zai Ba Wa Maniyyatan Hajjin Bana Tallafin Naira Dubu 500


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana amincewar gwamnatinsa na rage wa maniyyatan hajjin bana naira dubu 500 bayan da Hukumar Alhazan Najeriya ta kara naira miliyan 1.9 akan kudin hajjin bana.

WASHINGTON DC - Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, wadda a da aka fi sani da Tuwita, inda yace:

“Sakamakon karin kudi har kimanin Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000) da Hukumar Alhazan Najeriya ta yi akan kowacce kujerar aikin Hajji, ina farin cikin sanar da dukkanin maniyyatan jihar Kano cewar Gwamnatin Kano ta musu ragin Naira dubu dari biyar (500,000) akan kowacce kujera.

Sanarwar ta kara da cewa " Wannan ragi da muka samar a yanzu haka na nufin duk wani maniyyaci da ya biya naira miliyan hudu da dubu dari bakwai (4,700,000) kudin babbar kujera da wadanda suka biya naira miliyan hudu da dubu dari biyar (4,5000,000) kudin karamar kujera za sucika Naira miliyan daya da dubu dari hudu (1,400,000) ne kacal maimakon Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000).

A watan Fabrairu da ya gabata ne Hukumar ta kara kudin aikin hajjin 2024 yayin da darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kan dalar Amurka.

Tun da farko hukumar ta sanar da Naira miliyan 4,500,00 a matsayin kudin aikin hajjin 2024, amma yanzu kudin ya kama daga Naira miliyan 4,999,000 daga kudanci zuwa Naira miliyan 4,699,00 a arewa, yayin da a arewa maso gabas, Maiduguri da Yola mafi kusanci da Saudiyya ya ke Naira 4,679,000.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG