Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazai Ta Kasa A Najeriya Ta Nemi Bukatar Shiga Kasuwar Dabbobi Na Aikin Hajji A Saudiyya


Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta bukaci bankin cigaban Musulunci da ya baiwa Najeriya damar shiga kasuwannin Saudiyya na cinikayya da hada-hadar sayen dabbobin da ake amfani da su a lokacin ibada na aikin Hajji.

Shugaban Hukumar, Aliyu Jalal ya gabatar da bukatar ne a ziyarar da ya kai a baya bayan nan don neman samar da wata kafa na bunkasa kasuwanci da samar da kudin shiga ga kasa ta hanyar fitar da dabbobin hadaya daga Najeriya izuwa Saudiyya.

Baya ga neman hanyar shiga kasuwar dabbobi, Shugaba Jalal ya jaddada irin gudunmawar da kwararrun ma’aikatan Najeriya za su iya bayarwa, da suka hada da likitocin dabbobi da ma’aikatan aikin hannu wajen gudanar da ayyuka a lokacin aikin Hajji, musamman a lokacin da ake aiki na hadaya.

Bukatar tana da nufin haɓaka haɗin gwiwa ta hanyar shigar Najeriya cikin muhimman abubuwan da suka shafi kasuwanci da aikace-aikace na aikin hajjin shekara-shekara.

A yayin taron, Shugaba Jalal ya bayyana jin dadinsa ga taimakon fasaha da mataimakin shugaban ayyuka na bankin cigaban Musulunci, Dakta Mansur Mukhtar, ya bayar a shekarar 2019.

Jalal ya bayyana irin gudunmawar da tallafin ya bayar wajen taimakon samar da tsarin ceto na ayyukan aikin Hajji da inganta harkokin Cibiyar Hajji ta Najeriya, in da ya ce shirye-shiryen ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa fannin aikin Hajji a Najeriya.

Bugu da kari, Shugaban ya ce hukumar ta NAHCON na ci gaba da kokarin zakulo hanyoyin da za a yi amfani da su wajen yi wa alhazan Najeriya hidima.

A tattaunawarsa da mataimakin ministan aikin hajji na Saudiyya, Dakta. Abdulrahman Bejawi, Shugaba Jalal ya nemi tabbaci dangane da jin dadin alhazan Najeriya da kuma kare dukiyoyinsu.

Haka zalika, a halin da ake ciki Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin kwamitin mutane 12 na hukumar NAHCON har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da hakan.

Shugaban a cikin kudurinsa na tabbatar da ayyukan Hajji na 2024 ba tare da wata matsala ba, ya kuma sabunta nadin Jalal Arabi a matsayin Shugaban Hukumar.

Sauran mambobin hukumar ta NAHCON, kamar yadda wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a jiya, sun hada da Aliu Abdulrazaq, kwamishinan tsare-tsaren ayyuka, ma'aikata, da kudi; Prince Anofi Elegushi, kwamishinan ayyuka da kuma Farfesa Abubakar Yagawal kwamishinan tsare-tsare da bincike.

Wakilan shiyyar sun hada da: Dr. Muhammad Umaru Ndagi, Arewa ta tsakiya; Abba Jato Kala, Arewa maso Gabas; Sheikh Muhammad Bin Othman, Arewa maso Yamma da Tajudeen Oladejo Abefe, Kudu maso Yamma.

Sauran su ne Aishat Obi Ahmed, Kudu maso Gabas; Zainab Musa, Kudu maso Kudu; Farfesa Musa Inuwa Fodio, Jama’atul Nasril Islam da Farfesa Adedimeji Mahfouz Adebola, Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci.

Shugaban ya umurci wadanda aka nada da su sadaukar da kansu wajen ganin ayyukan Hukumar Alhazai ta kasa ya kasance cikin inganci, gaskiya, gagarumar nasara da kuma biyan bukatun ‘yan Najeriya.

~Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG