Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NAHCON Ta Ce Za A Yi Amfani Da Sararin Samaniyar Sudan Wajen Jigilar Alhazai A 2024


Hajj House NAHCON, Abuja
Hajj House NAHCON, Abuja

Shugaban Hukumar NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke bitar matakan da hukumar ke dauka don tunkarar aikin hajin da ke tafe na shekarar 2024.

Ba kamar yadda ya faru ba a 2023, wanda sakamakon rikicin da a ke yi a Sudan tsakanin shugaban gwamnatin kasar Janar Abdulrahman Burhan da shugaban sojojin sa kai Janar Hamdan Hemedti Dagolo ya sa aka yi zagaye, a 2024 za’a bi ta sararin samaniyar Sudan.

NAHCON - Saudiyya
NAHCON - Saudiyya

A shekarar da ta gabata abun ya kai ga sai da aka yi amfani da wasu daga cikin kudin guzurin maniyata, saboda zagayen da a ka yi ya jawo karin kudin kujerar.

Shugaban Hukumar alhazai ta NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi ya bayyana cewa badi ba za’a fuskanci wannan kalubalen ba.

Shugaban Hukumar Malam Jalal Ahmed Arabi
Shugaban Hukumar Malam Jalal Ahmed Arabi

Duk da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki a Najeriya kuma ana shirin rufe karbar kudin a wannan watan, shugaban hukumar NAHCON yace ana samun nasara wajen karbar kudin kujerar da suka kai Naira miliyan 4.5.

Shugabar kamfanin Dija Travel, daya daga cikin kamfanonin jirgin yawo da zasu yi aikin hajjin 2024, Hajiya Amina Ibrahim Yusuf, ta ce zasu hada karfi da karfe da sauran kamfanoni don gudanar da aikin.

Hajiya Amina Ibrahim ta kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta duba lamarin farashin dala domin maniyata su samu sauki wajen biyan kudin kujerar.

Hukumar NAHCON dai ta sha alwashin inganta ayyukanta domin jin dadin alhazai.

Saurari rahoton Hauwa Umar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG