Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Kano Ya Nada Sababbin Sarakuna A Rano, Karaye Da Gaya


Sabon Sarkin Karaye
Sabon Sarkin Karaye

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada sababbin Sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Karaye, Rano da kuma Gaya.

A wata sanarwar da ya fitar mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce sababbin Sarakunan masu daraja ta biyu sun hada da Sabon Sarkin Karaye Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, wanda kafin nadin, shi ne Hakimin Rogo.

Sanarwar ta ce Alhaji Muhammad Isa Umar shi ne sabon Sarkin Masarautar Rano mai daraja ta biyu, wanda kafin nadin, shi ne Hakimin Bunkure.

Sai kuma sabuwar masarautar Gaya, wacce aka bai wa Alhaji Aliyu Ibrahim, wanda a baya shi ne ke rike da mukamin Sarkin Gaya kafin a rushe.

Nadin na su zai fara aiki nan take, a cewar sanarwar.

Sabon Sarkin Rano
Sabon Sarkin Rano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taya sababbin sarakunan masu daraja ta biyu murnar nadin, tare da yin kira a gare su da su yi aiki tukuru, don ganin sun kawo wa yankunan ci gaba da ake bukata.

Gwamnan Kano ya rattaba hannun a kan sabuwar dokar da ta kirkiro sababbin masarautun masu daraja ta biyu guda uku a ranar Talata 16 ga watan Yuli na 2024.

Sabuwar masarautar Rano da ta hada da kananan hukumomin Rano, Kibiya da kuma Bunkure. Masarautar Gaya ta kunshi kananan hukumomin Gaya, Ajingi da kuma Albasu. Sai kuma masarautar Karaye mai kananan hukumomin Karaye da Rogo.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG