Gwamna Tanko Umar Al-Makura yayi alkawarin ne yayinda jama'ar jihar suka sake zabarsa wa'adi na biyu.
Ya shaidawa Murya Amurka cewa yadda jam'iyyarsa ta samu rinjaye a majalisar jihar a wannan karo to da yaddar Ubangiji mutanen jihar zasu ga wasu canje-canje da zasu inganta rayuwarsu.
Yace Allah cikin ikonsa sun sami nasara a zabukan da suka gabata. Yace samun 'yan majalisa goma sha takwas ya bashi kwanciyar hankalin tafiyar da gwamnatinsa saboda adawa zata ragu. Galabar da suka samu a majalisa zata sa su yi aiki tukuru yadda al'ummar jihar zasu samu cigaba fiye da da can. Canjin zai zo a gurguje domin babu tangarda tsakanin gwamnati da majalisa.
Shekaru hudu da gwamnati zata yi nan gaba zata mayarda hankali akan yadda rayuwar al'umma ta ke. Zasu duba su ga ayyukan da zasu yi su kyautata rayuwar talakawa. Zasu rage cin hanci da rashawa. Zasu kirkiro da ayyukan yi ma matasan da suka yi karatu amma basu samu aikin yi ba saboda su samu kyakyawar kwanciyar hankali. Wani abu kuma da gwamnati zata mayarda hankali akai shi ne gaggauta samar da zaman lafiya.
A lokutan baya gwamnatin Al-Makura ta sha shiga takun saka da 'yan majalisar jihar kasancewa yawancinsu a wancan lokacin 'yan PDP ne.
Wasu jama'ar jihar sun bayyana burinsu da abubuwan da suke son gwamnatin tayi.
Ga rahoton Zainab Babaji.