Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Borno Ya Yabawa Hukumar 'Yan Gudun Hijira UNHCR Ta MDD


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima

Kashim Shettima gwamnan jihar Borno ya yabawa hukumar Majalisar Dinkin Duniya ko MDD dake kula da 'yan gudun hijra da aka sani da suna UNHCR dangane da tallafin kayan gini da suka ba wasu da rikicin Boko Haram ya rabasu da muhallansu

Gwamnan ya yi yabon ne lokacin da ita hukumar UNHCR ta bada kayan tallafin wa wasu a garin Konduga da suka koma suna kokarin sake gina muhallansu.

Yace taimakon mutanen da basu da karfi su kimanin dubu biyu ba karamin taimako ba ne. Yace sun ji dadin irin taimakon. Dubu talatin da aka baiwa mutane dari uku a garin Konduga kadai da kuma kayan gini saboda haka gwamnan ya sake mika godiyarsa ga UNHCR da ma'aikatar gine-gine saboda adalcin da ma'aikatan suka nuna.

Shugaban hukumar ta UNHCR yace taimakon kankani ne amma na nuna murnarsu saboda kokarin da gwamnatin jihar ta keyi na sake gina jihar Borno.

Kwamishanan gine-gine na jihar yace akwai mutane dari biyar da suka anfana da tallafin UNHCR, daga karamar hukumar Gwoza, dari uku daga Konduga dari uku daga Mafa dari biyar daga Dikuwa dari biyar daga Damboa sai kuma dari daga karamar hukumar Bama.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG