Gwamna Wike dai ya ce ayyukan mutanen na haddasa barna ga yanayi da aka fi sani da 'black soot' a turance a jihar ta Ribas, inda ya ce hakan babban laifi ne.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi na musamman da ya yi wa al'ummar jihar ya kuma ya umurci shugaban ma’aikatan jihar Ribas da ya nemi Temple Amakiri, wanda ke zaman darakta a ma’aikatar makamashi, don yin bayani kan zargin tallafawa ayyukan fasa bututtun mai ba bisa ka'ida ba.
Haka kuma ya yi umarnin a mika shi ga ‘yan sanda domin bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.
Wike ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Ribas cewa gwamnatinsa ta kudiri aniyar ganin ta shawo kan wannan matsalar ta hanyar rugujewa tare da rurrufe duk wasu wuraren da ake tace danyen mai ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
Gwamnan ya kuma ayyana wasu mutane da ya yiwa lakabi da jagororin ayyukan tace danyen mai ba bisa ka’ida ba, da ya ce ana neman su ruwa a jallo.
Mutanen da gwamna Wike ke zargi sun haɗa da Azubike Amadi, wanda ke zaman kwamandan OSPAC na yankin Ogbogoro kuma shugaban yankin Akpor ta tsakiya na al’umman OSPAC, da wani mai suna India na al’ummar Rumuolumeni kuma shugaban kungiyar masu samar da man fetur don amfani da jiragen ruwa a masarautar Akpor.
Akawi kuma Okey wanda ke kula da hada-hadar mai a yankin Rumupareli, da Mista Anderson, wanda ke kula da ayyukan hada-hadar mai a yankin Ogbogoro, shugaba a yankin, Amadi Gift, Azeruowa na yankin Ogbogoro, da kuma Kingsley Egbula, wanda shi ma dan yankin Ogbogoro ne.
Haka zalika, gwamnan ya ayyana cewa ana neman wasu dake tace mai ba bisa ka’ida ba a yankin Isiokpo da suka hada da Kemkom Azubike, Mezu Wabali, Chigozi Amadi, Opurum Owhondah, Bakasi Obodo , Opus, Galaxi Mas, Mista Chioma, Mista Ogondah, Mista Soja, Mista Chefo, da kuma Nkasi.
Gwamna Wike ya ce gwamnatinsa ta kuma gano wadanda ke da hannu a ayyukan tace danyen mai ba bisa ka'ida ba a yankunan Okrika, Garin Fatakwal, Ribas ta kudu maso gabas da kuma Ribas ta kudu maso yamma, inda ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a buga sunayensu tare da bayyana neman su ruwa a jallo, idan har suka ki daina ayyukansu da kuma kai kararsu ga ‘yan sanda.
Wike ya kuma kara da sake jadada cewa, dokar hana amfani da babura gaba daya a kananan hukumomin Obio/Akpor da Fatakwal na aiki har yanzu, matakin da gwamnati ta dauka sakamakon barazanar da suke yi ga tsaron rayuka da dukiyoyi al’umman yankin.