Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Jihar Neja Yayi Allah Wadai da Kona Motar PDP

Mua'zu Babangida Aliyu Gwamna Jihar Neja.
Mua'zu Babangida Aliyu Gwamna Jihar Neja.

Shugaban kungiyar Gwamnonin arewacin Najeriya, Gwamna Mua’zu Babangida Aliyu, na jihar Neja, yayi Allah wadai da matakin da wasu suka dauka na kona motocin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan, a jihar Filato.

Gwamnan yayi wannan suka ne a lokacin da yake jawabi a wata ziyaran sasantawa, a tsakanin ‘ya’yan jamiyyar PDP, da shuwagabanin ta na arewa maso tsakiyar Najeriya, da suka kai masa a gidan Gwamnati a Minna.

Yace ya sama tilas “muyi Allah wadai da abunda ya faru a jihar Filato, inda harka kawai mutane daga ganin motoci da alama suka kona, dole ne mu dauki matakin ganin irin haka bai sake faruwa ba.”

Mataimakin shugaban jamiyyar PDP, a Najeriya, mai kula da yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, Yusuf Ajitogo, yace duk da yake sun zo sasantawa ne a jihar Neja amma tabbas duk wanda ya ci amanar jamiyyar ta PDP, toh fa amana zata ci shi.

Gwamna Jihar Neja Yayi Allah Wadai da Kona Motar PDP - 2'46"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG